Nevada jiha ce daga jihohin ƙasar Tarayyar Amurka,[1] dake yammacin ƙasar Amurka. Ta hada iyaka da Oregon daga arewa maso yamma, Idaho daga kudu maso gabas, birnin California daga yamma, Arizona daga kudu maso gabas, sannan kuma Utah daga gabas. Garin Nevada itace ta bakwai acikin jerin jihohi mafi tsaruwa a Amurka, itace ta 32 a yawan al'umma, kuma ta tara a karancin cunkuson al'umma a kasar Amurka. Mafi yawancin mutanen Nevada suna zaune ne a Clark County wacce ke dauke da yanki na kece raini wato Las Vegas–Paradise metropolitan area, wacce ta mamaye yankuna daga cikin birane hudu mafiya girma a kasar.[2] Babban birnin Nevada itace Carson City.Las Vegas itace birni mafi girma a Nevada.
Babban birnin jihar Nevada itace Carson City. Jihar Nevada na da yawan fili kimanin kilomita arabba’i 286,382, da yawan jama'a 3,060,150, Gwamnan jihar Nevada Steve Sisolak ne, daga zaben gwamnan a shekara ta 2018.